logo

HAUSA

Wakilin Sin ya gabatar da ra’ayoyi guda uku game da kare tsarin hana yaduwar makaman nukiliya

2024-07-29 10:33:20 CMG Hausa

A ranar 26 ga watan Yuli, wakilin kasar Sin ya ba da jawabi game da hana yaduwar makaman nukiliya a taro karo na biyu na kwamitin shiryawa na babban taron bincike da tattaunawa kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya karo na 11. Wakilin Sin ya bayyana cewa, a halin yanzu, wasu kasashe masu makaman nukiliya sun tsaya tsayin daka kan ra’ayin yakin cacar baki, da yin gasa a tsakanin manyan kasashen duniya, lamarin da ya sa, suke nuna fuska biyu kan batun hana yaduwar makaman nukiliya, yayin da suka mai da moriyarsu na siyasa a gaban tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na kasashen duniya, hakan ya haddasa karin barazanar yada makaman nukiliya.

Wakilin Sin ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, ya kamata gamayyar kasa da kasa su cimma matsaya daya kan ka’idar kiyaye tsaro cikin hadin gwiwa, da kuma yin amfani da wannan dama don yin bincike da tattaunawa kan yarjejeniyar, wajen kara karfi da amfanin tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa. Sabo da haka, kasar Sin ta gabatar da ra’ayoyi guda uku, wato da farko, a daina aiwatar da matakan da za su rage karfin tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa. Na biyu shi ne, a warware matsalolin dake janyo hankulan jama’ar yankuna ta hanyar siyasa da diflomasiyya. Daga karshe dai, a dukufa wajen kiyaye da kara karfin tsarin hana yaduwar makaman nukiliya na kasa da kasa. (Mai Fassara: Maryam Yang)