logo

HAUSA

Wanda ya shuka zamba, shi zai girbe ta

2024-07-29 21:56:51 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

“Mun yi karya da yaudara da sata, mun kuma samar da darussa na musamman na koyar da ayyukan, wadanda suka kasance abubuwan da muke alfahari da su na tabbatar da ci gaban kasar Amurka.” Kalaman tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ke nan, don gane da irin abubuwan kunya da Amurka ta aikata ba tare da boyewa ba a shekarun baya. Lallai a kan batun yaudara, Mr.Pompeo ya fadi gaskiya.

A kwanan nan kuma, a karon farko cikin shekaru 12, rundunar sojin Amurka ta wallafa tsarin tafiyarwa mai lakabin "Yaudara", wato wani salo da ake amfani da shi wajen yaudarar abokan gaba da kitsa karairayi, matakin da ya ba kasashen duniya mamaki matuka.

A hakika, domin cimma burinta, har kullum Amurka ba ta jin kunyan aikata karya da yaudara da kuma sata, a maimakon haka, tana alfahari da su. Kuma ba a fannin soja kawai Amurka take yaudara ba, ma iya cewa hakan ya zame wa kasar jini da tsoka. Idan ba mu manta ba, a tsakiyar karni na 20, hukumar leken asiri ta CIA ta Amurka, ta fara aiwatar da shirin da aka san shi da suna “Operation Mockingbird”, shirin da ke yunkurin sayen ’yan jarida da wasu hukumomin kasa da kasa don samun bayanan sirri, kuma har zuwa yanzu, kana hukumar CIA ita ma tana kokarin sarrafa kafofin yada labarai ta hanyar sayen ma’aikatansu.

Kaza lika a shekarar 2003, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka Colin Powell, ya zargi kasar Iraki da nazari kan makamai masu guba, tare da nuna farin garin da ya samu a gun taron kwamitin sulhun MDD, kuma da wannan dalili ne sojojin hadin kai na Amurka da Birtaniya, suka kaddamar da yaki a kan Irakin, amma har zuwa yanzu, Amurka ba ta iya nuna hakikanin shaida mallakar makaman kare dangi a Iraki ba.

Ban da haka, Amurka ta kaddamar da yaki a kan Syria, bisa dalilin wai sojojin gwamnatin kasar sun yi amfani da makamai masu guba, amma ga shi sojojin kasar Amurka da ke Syria na satar albarkatun mai da alkama na Syria a kowace rana, tare da yin jigilarsu zuwa ketare.

Domin dakile kasar Sin kuma, Amurka ta yayata karairayi na shafa wa kasar bakin fenti, a kan manufofinta game da jihar Xinjiang, har ma ta yada karairayi game da alluran rigakafi da kasar Sin ta samar a yayin da ake fama da annobar COVID-19, ba tare da yin la’akari da lafiyar al’ummar kasashe masu tasowa wadanda ke tsananin bukatar rigakafin ba.

Irin wadannan abubuwa ba za su lissafu ba, wadanda suka kasance shaida ta “karya da yaudara da sata” da ’yan siyasar Amurka suka bayyana. Don haka abun tambaya a nan shi ne wace ce ke yada karairaiyi a fadin duniya, kuma wace ce ke gudanar da ayyuka na gurgunta fahimtar al’umma a kan wasu kasashe, kana kuma wace ce ke ta kutsen yanar gizo? Kasashen duniya sun san amsar hakan, kuma Amurka ta ci amana ta hanyar aikata munanan abubuwa.

Kamata ya yi Amurka ta daina yada karairayi, ta daina yaudarar al’ummar kasashen duniya, kuma ta daina shafa wa sauran kasashe kashin kaji. Kamar yadda Bahaushe kan ce, wanda ya shuka zamba, shi zai girbe ta!(Mai Zane: Mustapha Bulama)