logo

HAUSA

An kaurar da mutane dubu 3 sakamakon fashewar madatsar ruwa a gundumar Xiangtan ta Sin

2024-07-29 11:06:00 CMG Hausa

Da misalin karfe 8 na daren jiya Lahadi, madatsar ruwa ta Sixin dake garin Yisuhe na gundumar Xiangtan ta lardin Hunan na kasar Sin ta fashe, hadarin da ya haddasa illa ga gonaki da gidaje na manoman dake zama kusa da wurin. Bayan aukuwar hadarin, masu aikin ceto sun yi gaggawar zuwa wurin domin aiwatar da ayyukan ceto da kuma kaurar da mutane zuwa wuraren dake da tsaro.

Ya zuwa safiyar yau Litinin, sojoji sama da dari 6 na rundunar soja dake lardin Hunan dauke da kananan jiragen ruwa kimanin guda 60, sun tafi wurin domin gudanar da aikin ceto cikin gaggawa, yayin da masu aikin ceto sama da dari 2 daga kamfanin gine-gine na Anneng na kasar Sin suka je wurin tare da na’urorin musamman kimanin guda 110. Kana, kamfanin layukan dogo na CREC ya tura mutane guda 30 da manyan na’urori guda 4 zuwa wurin, haka ma kungiyar aikin ceto ta Blue Sky da kungiyar aikin ceto na wurin duk sun hallara a wurin da hadarin ya auku domin ba da taimako yadda ya kamata.

Ya zuwa yanzu, an riga an kaurar da mutane sama da dubu 3 zuwa wuraren dake da tsaro, kana, ba wanda ya ji rauni ko rasa ransa.

Bugu da kari, a halin yanzu, ana ci gaba da aikin kaurar da mutane da aikin ceto da kuma aikin kawar da hadari a wurin. (Mai Fassara: Maryam Yang)