Masu tsara unguwanni na dukufa wajen karewa da sake gyara lokunan Hutong a Beijing
2024-07-29 13:43:17 CMG Hausa
A yankin Dongcheng na birnin Beijing, hedkwatar mulkin kasar Sin, akwai wata tawaga ta matasa dake dukufa wajen karewa da sake gyara lokunan cikin birnin da ake kira da Hutong da harshen Sinanci, da kuma inganta muhallin rayuwar mazauna Hutong.
Tawagar ta hada da masu tsara unguwanni daga cibiyar tsarawa da fasalta birnin Beijing, kuma kaso 62 bisa dari na mambobin tawagar mata ne. A idanunsu, kowanne bulo da cimintin tangaran dake hutong, abu ne mai daraja.
Hutong wani nau’i ne na loko. Ana samun hutong a biranen arewacin kasar Sin, a kan jera su ne tare da haraba mai kusurwa 4. Hutong wani muhimmin bangare ne dake cikin tsarin birnin Beijing, kuma kasantuwarsu sun shafe tsawon karnuka.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, an aiwatar da ayyukan farfadowa da kare asalin sigar harabar gidajen, da kokarin inganta ababen more rayuwa domin kyautata rayuwar mazauna hutong.
Zhao Xing ita ce mai tsara fasalin unguwanni kuma mataimakiyar shugaban dakin nune-nunen tsarin Beijing. Ta fara kaunar aikin ne kusan shekaru 10, a lokacin da take taimakawa wajen tsara aikin kare tarihi da gine-ginen al’adu dake yankin Dongcheng.
Zhao da sauran mambobin tawagarta sun kasance gaba-gaba a aikin tsara unguwa, sun gudanar da ayyukan sake gyara wuraren jama’a sama da harabobi 30, sun inganta sama da kananan lambuna 20 a cikin unguwanni, kuma sun shirya daruruwan shirye-shiryen wayar da kan jama’a don gane da tsarawa da fasalin birni.
A Shijia Hutong aka yanke cibiyar ilimin zamani, kuma nan ne mahaifar dakin nune-nunen wasanni na jama’a na Beijing. A baya, fitattun murubuta da masana adabi na gida da wajen Sin ne ke zaune a wurin ko aiki ko ziyartarsa. Wata haraba mai lamba 24, ita ce ta zama hutong na farko mai lakabin gidan adana kayayyakin tarihi wato gidan adana kayayyakin tarihi na Shijia Hutong.
A shekarar 2011, gwamnatin yankin Dongcheng ta dorawa cibiyar tsarawa da fasalin birnin Beijing, alhakin tsarawa da kare gidan tarihi da gargajiya na Dongsi ta kudu. A kuma lokacin, Zhao ta ziyarci Shijia Hutong a karon farko, a nan ne kuma ta fara sha’awar tarihi da al’adun harabobinsa.
Bayan kammala tsara daftarin, Zhao da abokan aikinta suka yanke shawarar amfani da kwarewarsu na inganta muhallin rayuwa da gina karin wurare domin mazauna. Shawarwarin da suka bayar, sun samu goyon baya daga karamin ofishin yankin na Chaoyangmen, tun daga lokacin ake gayyatarsu a kai-a kai, domin shiga aikin karewa da sabunta Shijia hutong da sauran hutong dake kusa da shi.
Tawagar ta gano muhimmancin shigar da mazauna cikin aikin kare harabobin na gargajiya. Don haka, Zhao da tawagarta sun inganta kafa kungiyar al’umma ta kare Hutong, wadanda suka hada da mazauna da hukumomi da masu harabobin.
Baya ga ba ta matsayin sakatare janar na kungiyar, Zhao ta zama daya daga cikin masu kula da tsara unguwa a yankin.
Daga baya, adadi mai yawa na kwararrun masu tsara birane sun hada hannu da Zhao, domin kare yankunan hutong da al’adunsu.
A matsayin kwararriyar mai tsara fasali, Zhao ta san yadda za ta tuntubi mazauna yadda ya kamata, musamman yadda za ta shigar da su cikin aikin inganta muhallin harabobi.
Zhao da abokan aikinta sun ziyarci mazaunan, sun zauna da su domin tattauna hanyoyin inganta muhallin da suke rayuwa da kuma kirkiro wuraren amfanin jama’a.
Misali, saboda kokarin tawagar, wani dattijo a Yanyue hutong, ya amince ya cire wani gini da aka yi ba bisa ka’ida ba, wanda aka gina a kusa da wata mashigar wata haraba. A madadinsa, an kafa teburin wasan dara da furanni masu kyau da hanyar keken guragu. Wadannan kananan sauye-sauye sun samar da sauki sosai ga mazauna wurin, kuma sun inganta zamantakewa.
Zhao da abokan aikinta sun hada hannu da mazaunan wajen sake fasali da gina kananan lambuna a harabobin.
Yayin sake fasali da farfado da hutong, Zhao da abokan aikinta sun gano cewa, dole ne mutane su kasance jigon kare hutong, kuma yana da matukar muhimmanci su samu tarihin abubuwan tunawa masu daraja ga dattawan hutong, yayin da suke kokarin kare shi.
Domin adana tarihin hutong da na dattawan, Zhao da abokan aikinta sun kaddamar da wani aiki na tarihin baka. Sun tsara masu aikin sa kai su ziyarci mazauna tare da tattara labaran rayuwarsu a hutong. A sannan, gidan adana kayayyakin tarihi na hutong ya tsara wani shirin gabatar da tsoffin hotuna. An karfafawa mazauna nuna tsoffin hotunansu, ta yadda za a iya sake yin hotonsu domin gabatarwa yayin nune-nunen hotuna. Nune-nunen sun ja hankalin baki da dama musamman mazauna da suke son tuna baya, ta hanyar hotunan masu launin baki da fari, na tsohon hutong.
Irin wadannan ayyuka na sanya jama’a tuna abubuwa masu ban sha’awa da suka faru da bayyana sha’awarsu ga ingantacciyar rayuwa a nan gaba.
Zhao ta tuna yadda rukunin dattawa mazauna wurin suka taba shirya liyafar haduwa da abokan karatunsu, a wani gidan adana kayayyakin tarihi, domin murnar cika shekaru 60 da kammala makarantar firamare ta Shijia. Zhao ta bayyana cewa, “sun bayar da labaran abubuwan da suka faru a lokacinsu na yaranta a hutong. Sun ce sun ji dadin lokacin yarantarsu a hutong. Bisa samun kwarin gwiwa daga labaransu, mun shirya wani nune-nune a dakin tarihin wanda ya mayar da hankali kan tattaunawa tsakanin dattawa da yara, game da gina unguwar da za ta dace da yanayin rayuwar yara.”
Sama da rabin mambobin tawagar Zhao mata ne, kuma cikin shekaru da dama, sun bayar da gudunmuwa ta musamman wajen kare hutong. Sun taimakawa gidan adana kayayyakin tarihi na Shija hutong, wanda yanzu ya zama wajen misali na rayawa da kare tsoffin birane. Gidan tarihin ya samu karbuwa sosai, kuma yana samun masu ziyara daga ciki da wajen kasar Sin da yawansu ya zarce 120,000 a kowacce shekara.
A cewar Zhao, gidan tarihin na gabatar da kwarjinin al’adun yankunan hutong a Beijing, kuma ya zama wani dandali da mazauna ke haduwa a dama da su cikin aikin kare yankunansu da inganta muhallin rayuwa.
Gidan tarihin na kuma kokarin hada dukkan bangarorin rayuwa kamar daliban kwalejoji da jami’o’i, da cibiyoyin kwararru, da masana, da masu sha’awar al’adu, domin taimakawa wajen kare gine-ginen tarihi da al’adu.
Zhao ta nuna cewa, “mazaunan na rayuwa cikin jin dadi, an inganta muhallin tsohon birnin, kuma an raya al’adu. A ganina, wannan shi ne abun da ya kamata masu tsara birane su yi. Babban burinmu shi ne, samar da kyawawan sauye-sauye a unguwannin, da tafiya tare da tsarin ci gaba na sabon zamani, ta yadda mazauna za su ji cewa, sun samu farin ciki da tsaro.” (Kande Gao)