Shugaban addinin Iran ya nada Pezeshkian a matsayin sabon shugaban kasar
2024-07-29 10:41:58 CMG Hausa
A jiya Lahadi, shugaban addinin kasar Iran Ali Khamenei ya nada Masoud Pezeshkian a matsayin shugaban kasar na tara.
A yayin wani bikin da aka gudanar a Tehran, fadar mulkin kasar Iran, Khamenei ya sa hannu kan kudurin nadin da shugaban rikon kwarya Mohammad Mokhber ya gabatar, gami da mika takardar ga Malam Pezeshkian, don sanar da nada shi a matsayin shugaban kasar Iran a hukumance.
A ranar 6 ga watan Yuli ne aka tabbatar da Masoud Pezeshkian a matsayin shugaban kasar Iran, bayan nasarar da ya samu a takarar da ya yi da Saeed Jalili, tsohon babban jami'i mai kula da aikin shawarwari kan maganar nukiliya. (Bello Wang)