logo

HAUSA

Lambobin mallakar fasaha miliyan 4.425 ne ke aiki a kasar Sin

2024-07-29 11:04:51 CMG Hausa

A yau, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai kan "Sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko". A gun taron, darektan ofishin kula da ikon mallakar fasaha na kasar Sin Shen Changyu, ya gabatar da yanayin da ake ciki gama da lambobin mallakar fasahar kirkire-kirkire a kasar Sin.

Ya ce, ya zuwa watan Yunin bana, akwai lambobin mallakar fasahar kirkire-kirkire har miliyan 4.425 a kasar Sin masu aiki. Daga cikinsu, adadin lambobin mallakar fasahar kirkire-kirkire wadanda mamallakansu masu kamfanoni ne ya karu zuwa kashi 72.8 cikin dari, lamarin da ya nuna cewa, ayyukan kirkire-kirkire na kamfanonin kasar Sin sun kara kaimi.

Ban da wannan kuma, adadin lambobin mallakar fasahar kirkire-kirkire masu kima da daraja a cikin mutane 10,000 na kasar Sin ya kai kashi 12.9 cikin dari, inda aka cimma burin da aka sanya gaba na tsare-tsaren kasar Sin masu dacewa kafin lokaci. (Mohammed Yahaya)