‘Yan wasan alkafura cikin ruwa na Sin sun lashe gasar ajin maza daga tudun mita 10 a gasar Olympics ta Paris
2024-07-29 21:11:44 CMG Hausa
‘Yan wasan alkafura da tsunduma cikin ruwa na Sin Lian Junjie da Yang Hao, sun lashe lambar zinari ta wasan ajin maza daga tudun mita 10, a gasar Olympics ta Paris dake gudana yanzu haka.
Lian da Yang, sun kai ga cimma wannan nasara ne a Litinin din nan, ko da yake tun a baya suna rike da kambin duniya guda 3 na wasan, amma wannan ne karon farko da suka cimma nasarar lashe lambar zinari a gasar Olympic. (Saminu Alhassan)