logo

HAUSA

Han Zheng ya gana da shugaban kwamitin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach

2024-07-28 21:19:28 CMG Hausa

Da yammacin jiya Asabar 27 ga watan nan, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban kasar Han Zheng, ya gana da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach a birnin Paris na kasar Faransa.

Da farko Han Zheng ya isar da gaisuwar shugaba Xi Jinping ga shugaba Bach, inda ya ce, bikin bude gasar wasannin Olympics na birnin Paris ya yi matukar kayatarwa, kuma an samu cikakkiyar nasara wajen shirya bikin, bangaren kasar Sin ya taya shi murna kan hakan.

A cewarsa, wasannin motsa jiki na Olympics, na da nufin wanzar da zaman lafiya a duniya, da inganta hadin kai da ci gaban bil’adama. Bisa ga halin da ake ciki a duniya, yana da matukar muhimmanci a karfafa yada ruhin Olympics, don haka gasar wasannin Olympics a wannan karo tana da muhimmiyar ma’ana.

A nasa bangaren, mista Bach ya bayyana cewa, tushen imani na al’amuran Olympics na kasa da kasa, shi ne amincewa da ra’ayin bangarori da dama. A ko da yaushe kasar Sin tana goyon bayan al’amuran wasannin Olympics na kasa da kasa, ta kuma yi nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022, a yanayin musamman na yaki da COVID-19, wanda ya kasance abin koyi ga kasashen duniya, wajen samun nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics.

Bach ya kara da cewa, kwamitinsa yana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, don daukar nauyin shirya wasannin motsa jiki daban-daban na kasa da kasa, da kuma sa kaimi ga yada ruhin Olympics. (Bilkisu Xin)