logo

HAUSA

'Yan Nijar fiye da 400 aka tuso keyarsu daga kasar Libiya

2024-07-28 17:19:55 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ayyukan jin kai suka nuna damuwa game da dubban 'yan Nijar da aka koro daga kasar Libiya suka samu matsugunnin wucin gadi a birnin Dirkou, kungiyar jin kai ta Alarme Phone Sahara ta bayyana damuwarta tare da yin kira ga hukumonin Nijar da su gaggauta daukar matakan daukar nauyin wadannan mutane.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Kasar Nijar har kullum na fama da kwararar bakin haure daga arewacin kasar, musamman ma bakin haure da ake koruwa daga kasar Aljeriya baya bayan nan kuma daga kasar Libiya. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Alarme Phone Sahara ta bayyana cewa 'yan Nijar 463 aka tuso keyarsu a cikin tsakiyar watan Yulin shekarar 2024 zuwa birnin Dirkou da ke arewa maso gabashin kasar Nijar tun daga kasar Libiya. Haka kuma wannan kora ta gudana ba tare da sanar da hukumonin kasar Nijar ba da farko.

Azizou Chehou, shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam da aikin jin kai ta Alarme Phone Sahara ya bayyana a yanzu yana damuwa matuka da koruwar bakin haure cikin manyan biranen arewacin kasar. Domin wuraren karbarsu sun cika makil. Haka kuma zuwan wadannan mutane na tattare da illoli ga al'umomin wurin. Musamman ma ana lura da karuwar sace sace da kuma karuwanci.

A cewar Azizou Chehou, wadannan bakin haure 463 da suka zo ba zata, ya kawo wani rudani ga hukumonin wurin da ke neman sansanin da za'a tsugunar da su.

Dole a dauki matakan gaggawa domin magance wannan matsala, aiki da dokokin kasa da kasa na kare 'yanci da hakkin dan Adam. Kuma ya zama wajibi kasashen Aljeriya da Libiya su girmama mutuncin baki da ke cikin kasashensu, idan suka ci gaba da turo mutane zuwa wannan yankin Agadez, to za'a fuskanci matsalar jin kai mai tsanani, in ji shugaban kungiyar Alarme Phone Sahara. (Mamane Ada)