Mataimakiyar sakatare janaral na majalisar dinkin duniya Amina muhammad ta ziyarci shugaban tarayyar Najeriya a cigaba da rangadin kasashen ECOWAS
2024-07-28 16:27:51 CMG Hausa
Mataimakiyar sakatare janaral na majalisar dinkin duniya Amina Muhammed ta ce rangadin da take yi zuwa kasashen dake cikin kungiyar ECOWAS na kulla sabon kawance yana samun nasara sosai.
Ta tabbatar da hakan ne ranar Juma`a 26 ga wata lokacin da ta ziyarci shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu a fadar sa dake birnin Abuja, ta ce majalisar dinkin duniya na fatan kowacce kasa a nahiyar ta kasance bisa tafarkin demokradiyya.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mataimakiyar sakatare janaral na majalisar dinkin duniya ta shaidawa shugaban na tarayyar Najeriya cewa ta ziyarce shi ne domin yi masa bayani a kan sakamakon ziyarar da tawagarta suka kai kasashen Senegal da Guinea da Mali da jamhuriyyar Nijar da kuma Burkina-faso.
A zantawar ta da manema labaran fadar shugaban kasa, Hajiya Amina Muhammed ta ce sun kuma kai ziyara kasar Ethiopia a kan al`amuran da suka shafi kudi, sannan kuma sun tattauna da shugaban kasar a game da shawarar da ya gabatar da ita na cigaba da tattaunawa da wasu jahohin kasar da ake da matsala da su.
Ta ce a wasu kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS, al`umomin kasashen na kokawa sosai saboda yadda ake gudanar da sauye sauye a cikin kundin tsarin mulkin kasashen ba bisa ka`ida ba, inda ta kara nanata cewa wajibi ne irin wadannan kasashe su gaggauta komawa kan tsarin mulkin demokradiyya.
“Duk kasar da ta gabatar da taswirar tsare-tsarenta, da zai baiwa kowa kwarin gwiwa tare da gaskata komawa kan tafarkin demokuradiyya tabbas za ta samu goyon bayan majalissar dinkin duniya”
Ta yaba ta mutuka bisa kokarin kungiyar ta ECOWAS wajen hana wasu daga cikin mambobin kungiyar ficewa daga cikinta.(Garba Abdullahi Bagwai)