logo

HAUSA

Wang Yi ya gargadi Philippines game da tura makami mai linzami na Amurka

2024-07-27 15:52:50 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Phillippines Enrique Manalo a jiya Juma’a, inda ya gargadi bangaren Philippine kan matakin shigar da tsarin makami mai linzami na Amurka.

Wang ya ce, kasashen Sin da Philippines makwabta ne na kud-da-kud da teku ke raba su, kuma kyakkyawar makwabtaka, da hadin gwiwar moriyar juna, da samun ci gaba tare, su ne muhimman moriyar kasashen biyu.

Ya kara da cewa, idan kasar Philippines ta bullo da tsarin makami mai linzami na Amurka, to hakan zai haifar da tashin hankali da rikici a yankin, wanda kwata-kwata bai dace da muradun al'ummar Philippines ba. (Yahaya)