An shigar da layin da ya ratsa tsakiyar Beijing cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya
2024-07-27 15:28:11 CMG Hausa
Yau Asabar, a gun taron kayayyakin tarihi na UNESCO karo na 46 da aka gudanar a birnin New Delhi, babban birnin kasar Indiya, an shigar da "Layin da ya ratsa tsakiyar birnin Beijing wato tsarin babban birni mafi kyau na kasar Sin" da Sin ta gabatar a hukumance a cikin jerin kayayyakin tarihi na duniya. Kawo yanzu, yawan kayayyakin tarihi na duniya da Sin take da su ya kai 59.
Layin da ya ratsa tsakiyar birnin Beijing yana cibiyar tsohon garin Beijing, wanda tsawonsa ya kai kilomita 7.8, an fara gina layin ne a karni na 13, wanda ya tsara tsoffin gine-gine da wadanda suka ruguje bisa tsari na tsohon birnin, kuma ya kunshi jimillar abubuwan gargajiya guda 15. (Safiyah Ma)