logo

HAUSA

Firaministan Vanuatu: Tunanin al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya ya zo daidai da burin kasar Vanuatu

2024-07-27 15:24:45 CMG Hausa

A 'yan kwanakin da suka gabata, wakilin CMG ya yi hira da firaministan Vanuatu Charlot Salwai da ya yi ziyara a kasar Sin. Inda jami'in ya ce, a kasarsa ta Vanuatu, jama’a suna maraba da manufar gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil'adama, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ganin yadda manufar ta Sin ta zo daidai da buri da manufar raya kasa ta Vanuatu.

Ban da haka, babban jami’in ya ce, ba ma kawai kasar Sin ta taimaka wa Vanuatu wajen gina tashoshin jiragen ruwa da tituna ba, har ma tana tallafawa Vanuatu a lokacin da wasu bala'o'i suka afku, tare da ba da taimakon jinya ga makarantu da al'ummomin kasar. Ya ce yana godiya sosai da hakan.

Jami’in ya kuma nuna goyon bayansa ga daliban Vanuatu da su yi karatu a kasar Sin da koyon Sinanci, ya ce, ko shakka babu kasar Vanuatu za ta kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a nan gaba. (Bello Wang)