Wakilin Sin ya bukaci a tsagaita bude wuta a Gaza
2024-07-27 15:44:17 CMG Hausa
Zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong ya bayyana a jiya Juma’a cewa, bai kamata a ce babu ranar kawo karshen shawarwari na sasanta rikicin Gaza ba, kuma ya bukaci a tsagaita bude wuta a Gaza a kan lokaci.
Fu ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar a taron kwamitin sulhu na MDD kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da batun Falasdinu, inda ya ce, fiye da watannin tara ke nan ake ci gaba da gwabza rikici a zirin Gaza, wanda ya haifar da bala’in jin kai da ba a taba ganin irinsa ba, tare da asarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba kusa 40,000.
Ya kara da cewa, kusan watanni biyu ke nan da zartar da kuduri mai lamba 2735 na kwamitin sulhu, to amma Isra'ila ta ci gaba da gudanar da manyan ayyukan soji a Gaza, yana mai jaddada cewa, "Bai kamata a yi amfani da rayukan fararen hula a matsayin hanyar shawarwari na neman sasantawa ba." (Yahaya)