logo

HAUSA

An kaddamar da wasannin Olympics na Paris

2024-07-27 15:22:48 CMG Hausa

A ranar 26 ga watan Yuli, bisa agogon kasar Faransa, an gudanar da bikin bude gasar wasannin Olympics ta lokacin zafi karo na 33 a birnin Paris na kasar Faransa. A wajen bikin kaddamarwar da ya gudana, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar da bude gasar Olympics ta birnin Paris a hukumance.

Gasar Olympics ta lokacin zafi ta birnin Paris ta shekarar 2024 ita ce gasar irinta ta farko da birnin Paris na kasar Faransa ya karbi bakuncinta cikin shekaru 100 da suka wuce, bayan da birnin ya karbi bakuncin gasar sau biyu a tarihinsa wato a shekarar 1900 da ta 1924.

Wannan kuma shi ne karo na farko a tarihin gasar Olympics da ba a gudanar da bikin bude gasar a cikin wani filin wasa ba, yayin da 'yan wasa daga duk fadin duniya suka shiga kwale-kwale da yin fareti a cikin kogin Seine, inda suka wuce shahararrun wuraren tarihi na birnin Paris daya bayan daya. (Bello Wang)