Tawagar Sin ta samu lambar zinari ta farko a gasar wasannin Olympics ta Paris
2024-07-27 19:33:11 CMG Hausa
Yau Asabar, a gasar wasannin Olympics da ake yi a birnin Paris, an yi gasar cin lambar zinari ta wasan harbin bindiga mai nisan mita 10 ta tawagar gaurayawar namiji da mace, inda ‘yan wasan kasar Sin Huang Yuting da Sheng Lihao sun lashe gasar.
Wannan ita ce lambar zinari ta farko da aka samu a gasar wasannin Olympics ta Paris ta shekarar 2024, kuma lambar zinari ta farko da tawagar kasar Sin ta samu a gasar wasannin Olympics na wannan karo.(Safiyah Ma)