logo

HAUSA

Wang Yi ya halarci taron ministocin wajen ASEAN-Sin-Japan-ROK

2024-07-27 19:50:18 CMG Hausa

A ranar 27 ga watan Yuli agogon Vientiane, mamban ofishin siyasan kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron ministocin harkokin wajen ASEAN, Sin, Japan da ROK ko Koriya ta Kudu (10+3) a brining Vientiane na kasar Laos.

Wang Yi ya bayyana cewa, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da dukkan bangarori, da riko da gaskiya, da sa kaimi ga dunkulewar tattalin arzikin yankin, da tabbatar da burin kafa al’ummar gabashin Asiya.

A wannan rana har ila yau, Wang Yi ya kuma gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken a Vientiane bisa bukatarsa.

Bugu da kari, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin a yau ta gabatar da batun jigilar kayayyakin da Philippines ke yi wa jirgin ruwan yakin dake jibge a tudun ruwan Ren'ai, inda ta bayyana cewa, Philippines ta sanar da kasar Sin tukuna kafin ta yi jigilar kayayyakin. Kuma bangaren Sin ya ba da damar isar da kayayyakin bayan da ya tabbatar cewa kayayyakin jin kai ne kawai ake jigilar su. (Yahaya)