logo

HAUSA

Kasar Sin ta gina tsarin gargadin girgizar kasa mafi girma a duniya

2024-07-27 15:17:50 CMG Hausa

Wajen wani taron manema labarai da hukumar girgizar kasa ta ma'aikatar kula da agajin gaggawa ta kasar Sin ta gudanar a kwanan nan, an ce, an yi nasarar kammala aikin gina tsarin gargadin abkuwar girgizar kasa a kasar a ranar Alhamis 25 ga wata, aikin da aka kaddamar tun shekarar 2018, ta yadda kasar ta samu wani tsarin gargadin abkuwar bala’in girgizar kasa mafi girma a duniya.

Wannan tsarin gargadi ya shafi manyan tsare-tsare na fasahohi guda biyar, wato tsarin tashoshin sa ido, da na sarrafa bayanai, da tsarin samar da bayanan girgizar kasa cikin sauri, da tsarin sadarwa na musamman, da kuma tsarin samar da hidimar tabbatar da ingancin na'urori. Kana don gina wannan cikakken tsarin gargadi, an kafa cibiyoyin samar da gargadi 33, da tashoshin sa ido na nau'ika daban daban kusan 20,000, gami da tsarin tantance bayanai mai sarrafa kansa wanda aka kirkira a kasar Sin. Yayin da tsarin gargadin ke aiki, yana daukar matsakaicin tsawon lokacin wasu dakika 7 kacal don ba da gargadin abkuwar girgizar kasa a wasu wuraren da aka fi samun abkuwar bala'in. Saboda haka zai ba mutane kimanin dakika fiye da goma domin su kare kansu tare da tserewa, kafin karfin girgizar kasa ya fara yin barna a wuraren da mutane suke zaune. (Bello Wang)