logo

HAUSA

Jawabin shugaban CNSP, shugaban kasa Abdourahamane Tiani yayi albarkacin cikon shekara guda na mulkin soja

2024-07-26 19:04:25 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, a ranar yau Juma’a 26 ga watan julin shekarar 2024 ake shagulgulan cika shekara guda da zuwa sojoji kan karagar mulki, albarkacin wannan rana, shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP kana shugaban kasa birgadiye janar Abdourahamane Tiani ya gabatar da wani jawabi zuwa ga ‘yan kasa.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

A cikin jawabinsa ta hanyar gidan rediyo da talabijin na kasa zuwa ga ‘yan Nijar maza da mata, shugaban kasa, Abdrourahamane Tiani ya tabo muhimman batutuwan da suka shafi rayuwar kasa da al’ummar Nijar. Inda ya fara da cewa shekara guda ke nan da kwamitin ceton kasa na CNSP ya kama iko a karkashin jagorancina, bayan ya dauki niyyar ceto kasa daga cikin halin da ta shiga na rashin tabbas. Hakika cikin barazana ta kowane bangare da Nijar ta ke fuskanta, ya sanya duk wani mai kishin kasa ba da zai ba shi damar rufe ido ba, ya bar kasarsa ta fadi cikin tashin hankali da ta’addanci duk cewa kuma an bar sojojin kasashen yammacin duniya sun kafa sansanoninsu. Haka kuma cikin jawabinsa shugaban CNSP yayi allawadai da yadda aka yi ta satar albarkatun karkashin kasa, cin hanci da rashawa, da toshe ‘yancin dan adama, abubuwan da suka yi kamari a lokacin tsohon mulki. Juyin mulkin CNSP, juyin mulki ne da ‘yan kasa suka mai da juyin juya hali domin bayyana goyon bayansu ga sabbin hukumomin soja.

Ganin cewa aiki ne na ceton kasa da kuma kishin kasa baki daya. Hakan kuma a cewar shugaban kasa, ya taimako wajen korar sojojin Faransa daga kasar Nijar da korar jakadan kasar Faransa daga Nijar, haka kuma aka bukaci sojojin Amurka da su bar Nijar. Jawabin shugaba Tiani kuma ya maida hankali tare da jinjinawa kasashen Mali da Burkina Faso bisa kokarinsu na tsayawa tsayin daka wajen hada kai da Nijar, tare da kafa kungiyar kasashen yankin Sahel AES, da kuma janyewar kasashen uku da daga cikin kungiyar G5-Sahel da kuma kungiyar CEDEAO. A karshen wannan jawabi, shugaban CNSP ya tabo nasarorin da kasar Nijar ta samu a fuskar tattalin arziki, ci gaban al’umma duk da takunkumin CEDEAO da UEMOA bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan juli shekarar 2023. ‘Yan Nijar sun yi a jiki, dalilin wannan rashin gaskiya, amma suka nuna juriya da tashi tsaye domin kasancewa tsintsiya madaurinki daya tare da mambobin kwamitin ceton kasa da kuma gwamnatin rikon kwarya domin kai kasar Nijar da al’ummarta bisa tudun mun tsira, inji shugaban kasa Abdourahamane Tiani. Inda ya nuna daga karshe cewa makomar kasar Nijar na cike da fatan alheri don haka ya kara yin kira ga ‘yan Nijar da su sa kaimi wajen aiki tukuru da dogaro da kai, tare da kishin kasa da bautawa kasar domin bunkasa tattalin arziki da na al’umma da zaman lafiya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.