logo

HAUSA

An gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Rasha da Laos a karon farko

2024-07-26 16:06:18 CMG Hausa

Sin da Rasha da Laos, sun lashi takobin karfafa hadin gwiwa da kare tsaro da kwanciyar hankali a yankinsu. Kasashen 3 sun cimma wannan matsaya ce jiya Alhamis, yayin taro karo na farko na ministocin harkokin wajen kasashen, wanda ya gudana a birnin Vientiane.

Taron wanda mataimakin firaministan Laos kuma ministan harkokin wajen kasar Saleumxay Kommasith ya jagoranta, ya samu halartar ministan harkokin wajen Sin Wang Yi da na Rasha Sergey Lavrov.

Yayin taron, Wang Yi ya nanata muhimmancin karuwar tasirin kasashe masu tasowa a duniyar dake fama da kariyar ciniki da babakere da rikice-rikice a yankuna. Ya ce karfafa hadin kai tsakanin kasashen 3 ba muradunsu kadai zai kare ba, har da inganta kwanciyar hankali da wadata.

A nasu bangaren Sergey Lavrov da Saleumxay Kommasith, sun jaddada muhimmancin goyon bayan juna da ra’ayi iri guda da suke da shi kan manyan batutuwa, inda suka ce hadin gwiwar kasashen 3 za ta kasance mai alfanu ga jama’arsu. (Fa'iza Mustapha)