Mataimakin ministan wajen Sin ya kai ziyarar ban girma ga shugaban Najeriya
2024-07-26 19:56:57 CMG Hausa
A ranar 25 ga watan Yuli ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, ya kai ziyarar ban girma ga shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu a Abuja.
Chen Xiaodong ya ce, kasashen Sin da Najeriya sun samu sakamako mai kyau daga hadin gwiwar dake tsakaninsu a aikace, kuma suna kan gaba a wajen a dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika. A wannan kaka, za a gudanar da taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing. Kasar Sin na maraba da shugaba Tinubu domin halartar taron da kuma ziyartar kasar Sin.
A nasa bangare, Tinubu ya nuna jin dadinsa ga kasar Sin bisa yadda take mai da hankali da goyon baya ga ci gaban Afirka. Yana fatan kai ziyarar aiki a kasar Sin, da halartar taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da yin aiki tare da kasar Sin wajen sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a wani sabon mataki.
A wannan rana har ila yau, Chen Xiaodong ya kuma gana da ministan harkokin wajen Najeriya Maitama Tuggar. (Yahaya)