logo

HAUSA

Wata tawagar ministocin Jamhuriyar Nijar ta kai ziyara a Benin

2024-07-26 10:05:27 CMG Hausa

Wata tawagar manyan jami’an Nijar ta kai ziyarar aiki a birnin Cotonou na kasar Benin daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Yulin shekarar 2024, bayan da tawagar tsoffin shugabannin kasar Benin biyu suka kawo rangadi a birnin Yamai na kasar Nijar a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 2024. Manufar kasashen biyu ita ce ta kokarin daidaita rikicin da ke tsakaninsu.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

A filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Kadehon dake Cotonou, ministan cikin gida na kasar Nijar birgadiye janar Mohamed Toumba da darektan fadar shugaban kasa dokta Soumana Boubacar tare da rakiyar manyan jami’an tsaro na FDS sun samu tarbo daga tsoffin shugabannin kasar Benin biyu Nicephore Soglo da Boni Yayi. Muhimmiyar tawagar da shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP birgadiye janar Abdourahamane Tiani ya tura, ta yi tattaunawar farko tare da wadannan tsoffin shugabannin kasar Benin a falon tarbon baki dake filin jiragen saman kasa kasa, sannan kuma a otel inda aka sauke manyan bakin. Tattaunawar ta maida hankali kan halin dangantaka. Daga bisani, tawagogin biyu sun je fadar shugaban kasar Benin inda tawagar Nijar ta samu ganawa tare da shugaban kasar Benin Patrice Talon, nesa da ’yan jarida bisa tsawon fiye da sa’o’i biyu kan dangantaka tsakanin Nijar da Benin, kasashen dake makwabtaka da juna, da kuma iyakokinsu suke rufe, tare tsai da jigilar dayen man fetur.

Tawagar Nijar ta tattauna tare da ministan kasa dake kula da ci gaban ayyukan gwamnatin Benin, Abdoulaye Bio Tchiane a gaban idon ministan harkokin waje da ma’adinai. Tattaunawar da ita ma ta maida hankali kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da ke cikin mawuyacin hali, sa’o’i biyu na tattaunawa tsakanin bangarorin biyu kan batutuwan dake kawo ta da jijiyoyin wuya.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar