Kasar Sin ta yi kira ga dukkan bangarori dake da ruwa da tsaki a rikicin Ukraine da su nemi hanyar warware rikicin a siyasance
2024-07-26 11:54:51 CMG Hausa
Kasar Sin ta yi kira ga dukkan bangarori dake da ruwa da tsaki a rikicin Ukraine da su nemi hanyar warware rikicin a siyasance. Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Fu Cong ne ya yi kiran, yayin taron kwamitin sulhu kan samar da makamai ga Ukraine, inda ya ce warware rikicin a siyasance kuma da wuri, na da alfanu ga dukkan bangarori.
Ya ce yanzu haka ya kamata a mayar da hankali kan aiwatar da batutuwa 3, wato kada wani bangare ya fadada ko ta’azzara ko kara rura wutar yakin, domin shawo kan yanayin cikin hanzari.
Da yake jawabi game da ziyarar da ministan harkokin wajen Ukraine Dmytro Kuleba ya kawo kasar Sin, Fu Cong ya ce bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi game da rikicin. Kuma minista Kuleba ya ce Ukraine na girmama ra’ayin Sin, kuma ta nazarci shawarwari 6 da Sin da Brazil suka gabatar game da warware rikicin a siyasance, haka kuma a shirye Ukraine take ta tattauna tare da cimma yarjejeniya da Rasha. (Fa’iza Mustapha)