CMG ta kaddamar da motarsa ta nuna shirye-shiryen talibijin mai amfani da fasahar 8K a Paris
2024-07-26 11:45:24 CMG Hausa
Babban rukunin gidan rediyo da talibiiji na kasar Sin wato CMG ya kammala aikin girke na’urori da aikin gwajin tsarin nuna shirye-shirye na motarsa ta nuna shirye-shiryen talibijin mai amfani da fasahar 8K a filin motsa jiki na France dake Paris a jiya Alhamis, kuma motar ta an fara aiki da ita. Wannan mota da ake mata lakabi da “Jar kasar Sin” ta taba aiki a gasar Olympics ta Tokyo na Japan. A wannan karo ma, tana ci gaba da ba da tabbacin fasaha ga kamfanonin nuna shirye-shiryen wasannin gasar wato OBS a ketare, kuma karon farko, ta sauke nauyin dake wuyanta na sarrafa sakwanni ta fasahar 8K da kowa zai iya yin amfani da su a gasannin guje-guje da tsalle-tsalle da bikin rufe gasar a Paris.
A wannan rana kuma, shugaban CMG Shen Haixiong ya yi rangadi a filin don ganewa idonsa yadda aka share fagen wannan aiki, inda ya ce, aikin ba wakiltar sabon matsayin da CMG da dukkan kafofin yada labarai na Sin suke samu a bangaren nuna shirye-shiryen wasannin gasar kadai yake ba, har ma da bayyana cewa, ingantattun kimiyya da fasahar zamani da Sin ke rike da su na sahun gaba a duniya. (Amina Xu)