logo

HAUSA

Wakilin Xi zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Iran

2024-07-26 20:45:34 CMG Hausa

Yau Jumma’a, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a taron manema labarai cewa, bisa gayyatar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, Peng Qinghua, zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a birnin Tehran, babban birnin kasar, da za a gudanar a ranar 30 ga watan Yuli.

Ta kuma kara da cewa, kasar Sin za ta tura wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin yankin Turai da Asiya, Li Hui da ya ziyarci Brazil, da Afirka ta Kudu da kuma Indonesia daga ranar 28 ga watan Yuli, don gudanar da aikin diflomasiyya karo na hudu kan rikicin Ukraine, da kuma tattauna halin da ake ciki yanzu da kuma musayar ra'ayi kan tattaunawar zaman lafiya tare da wasu muhimman kasashe masu tasowa .

Bugu da kari, Mao Ning ta kuma gabatar da abubuwan da suka shafi ziyarar aiki da shugaban kasar Timor-Leste José Manuel Ramos-Horta ya kai kasar Sin nan ba da jimawa ba.

Ban da haka, ta jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ita ce zamanantarwa dake bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, kuma yadda kasar Sin ta tabbatar da zamanantarwa zai kara karfin zaman lafiya da ci gaba a duniya.

Ta kuma ce, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai gana da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a kasar Laos bisa gayyatar da ya yi masa. (Safiyah Ma)