Wang Yi ya gabatar da kyakkyawan sakamakon hadin gwiwar Sin da ASEAN
2024-07-26 19:20:14 CMG Hausa
A ranar 26 ga watan Yuli, agogon Vientiane, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar da sakamakon da aka samu a hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin Sin da ASEAN, yayin da ya halarci taron ministocin harkokin wajen Sin da ASEAN a Vientiane, babban birnin kasar Laos.
Ya ce, a fannin cinikayya, kasar Sin ta ci gaba da kasancewa kan matsayinta na babbar abokiyar cinikayyar ASEAN tsawon shekaru 15 a jere. Bugu da kari, adadin jiragen sama dake zirga-zirga kai tsaye tsakanin bangarorin biyu ya kai sama da jirage 2,300 a kowane mako guda.
Ya kuma bayyana cewa, ta fuskar hadin gwiwar masana'antu masu fasahohin zamani, ASEAN ta zama yankin da kamfanonin kera motoci na kasar Sin suka fi zuba jari a kasashen waje. (Yahaya)