logo

HAUSA

CMG ya gudanar da tattaunawa kan “Zurfafa gyare-gyare a Sin dama ce ga duniya” a Italiya da Jamus da Faransa

2024-07-26 14:11:20 CMG Hausa

 

An gudanar da taron tattaunawa tsakanin kasa da kasa kan “Zurfafa yin gyare-gyare a kasar Sin dama ce ga duniya” a Italiya da Jamus da Faransa. Kuma shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Wakilan kasashe 3 daga bangaren siyasa da kasuwanci da masanan ilmi da kafofin yada labarai sun tattauna kan ma’anar cikakken zama karo na 3 na kwamitin kolin JKS karo na 20 a birnin Beijing, da ma mu’ammalar al’adun Sin da Turai da damammakin da tsarin zurfafa gyare-gyare a Sin ke samarwa hadin kan Sin da Turai. (Amina Xu)