logo

HAUSA

Kamfanonin kasa da kasa fiye da 150 sun kulla yarjejeniya da bikin baje koli na CIIE a shekaru 7 a jere

2024-07-25 14:07:45 CMG Hausa

 

Da safiyar yau Alhamis aka gudanar da taron manema labarai game da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su Sin daga ketare wato CIIE karo na 7 da za a gudanar daga ran 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba a Shanghai.

An ba da labarin cewa, an kebe sassa 6 a wajen bikin, da kuma yankin gabatar da kayayyakin kirkire-kirkire. Ya zuwa yanzu, fadin yankin baje kolin ya kai fiye da muraba’in mita dubu 360, wanda kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 50 suka tabbatar da za su halarta a wannan karo.

A karon farko, kasashen Norway da Benin da Burundi da asusun kula da yara na MDD da sauran wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa za su halarci bikin. Bugu da kari, kawo yanzu, kamfanonin kasa da kasa fiye da 150 sun kulla yarjejeniya da bikin a cikin shekaru 7 a jere, kazalika wasu kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya ciki hadda Mitsubishi da NTT da sauransu za su halarci biki a karon farko. (Amina Xu)