logo

HAUSA

Firaministan Nijar ya jagoranci taron nazarin hadin gwiwa na ayyukan bankin duniya a Nijar

2024-07-25 10:35:07 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, firaministan din kasar Nijar kana ministan kudi da tattalin arziki, Ali Mahamane Lamine Zeine ya jagoranci taron nazarin hadin gwiwa na ayyukan bankin duniya a Nijar a ranar jiya Laraba 24 ga watan Julin shekarar 2024 a birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Taron nazarin ayyukan bankin duniya ya shafi duba ayyukan dake gudana, da duba halin yanayin ayyuka da ci gabansu, da tattauna muhimman kalubalen aiwatar da su da kuma gabatar da hanyoyin fita domin fuskantar kalubalen da aka tantance ta yadda a karshe za a kyautata ci gabansu.

Wadannan ayyuka dake gudana a Nijar guda 27 ne dake wakiltar fiye da miliyan 2500 na Sefa, daya daga cikin manyan ayyukan bankin duniya a nahiyar Afrika.

Wadannan ayyuka na shafar muhimman bangarorin da suka hada da ruwan sha, makamashi, noma, ilimi, sufuri, kiwon lafiya, gine-ginen ababen more rayuwa na jama’a da dai sauransu.

Kuma zuwa wannan rana, kashi uku daga cikin kashi hudu na wadannan kudade akwai su, kuma wadannan kudade da suke jiran a yi amfani da su sun wuce fiye da miliyan 1800 na Sefa.

Kuma kudaden da aka kebe domin gudanar da ayyukan da suka kunshi gine-ginen hanyoyin karkara, asibitoci, dakunan karatu, wuraren noman gandari, gine-ginen samar da makamashi, da horar da malaman makaranta, da samar da kayayyakin likita, da kayayyakin karatu da sayen magunguna da sauransu.

A cikin jawabinsa, firaminsita Ali Mahamane Lamine Zeine, ya bayyana jin dadinsa ga mahalarta taron da suka amsa kira da mai da hankali kan dangantakar kasar Nijar da sauran hukumomin kasa da kasa kamar bankin duniya, dake aiki domin kasarmu, musamman ma domin al’umomin kasashen da abin ya shafa, in ji Ali Mahamane Lamine Zeine. (Mamane Ada)