Jami’an MDD: Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya
2024-07-25 13:03:45 CMG Hausa
Tawagar wakilan dindindin ta kasar Sin dake MDD ta gudanar da liyafar murnar cika shekaru 97 da kafuwar rundunar sojan ’yantar da jama’ar Sin. Liyafar ta samu halartar manyan jami’an MDD da dama, inda suka yabawa muhimmiyar rawar da rundunar sojan Sin take takawa ga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD da ma tabbatar da kwanciyar hankali a duniya.
Mataimakin darekta mai kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na majalisar Jean-Pierre Lacroix ya bayyana cewa, har kullum, rundunar sojan kasar Sin tana ba aikin kiyaye zaman lafiya na majalisar goyon baya mai inganci, musamman ma a halin yanzu da ake fuskantar karin kalubaloli wajen aiwatar da aikin kiyaye zaman lafiya. Yana mai cewa, sojojin kasar Sin suna bayyana kwarewarsu da sadaukar da kai. Jami’in ya kuma yi fatan Sin za ta ci gaba da hadin kai da majalisar, don taka rawar gaggauta gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya. (Amina Xu)