CMG ya gudanar da tattaunawa kan “Zurfafa gyare-gyare a Sin dama ce ga duniya” a Najeriya
2024-07-25 20:43:46 CMG Hausa
A baya-bayan nan ne aka gudanar da tattaunawa kan “Zurfafa gyare-gyare a Sin dama ce ga duniya” a cibiyar al’adun kasar Sin dake birnin Abuja a Najeriya, wanda rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG da cibiyar raya al’adu ta kasar Sin suka shirya. Taron ya jawo manyan baki da masana wadanda suka gabatar da fahimta mai zurfi game da gyare-gyaren da kasar Sin ke yi da kuma tasirinsu a duniya.
An bude taron ne da jawabin mataimakin ministan yada manufofin JKS, kuma shugaban CMG Mista Shen Haixiong, inda ya jaddada muhimmancin ci gaba da yin hadin gwiwa tare da nuna godiya ga mahalarta taron.
Muhimman jawabai sun hada da bayani mai zurfi kan tasirin kasar Sin ga tattalin arzikin duniya, da muhimmiyar gudummawar da take bayarwa ga yanayin tattalin arzikin Najeriya daga bakin malama Fa'iza Mustapha. Yayin da Misis Patricia Naria, wacce ta wakilci mai girma ministan ma’aikatar yawon bude ido ta tarayya Najeriya, ta mayar da hankali kan bunkasa harkokin yawon bude ido a Najeriya da karfafa gwiwar matasa domin dakile kaura daga karkara zuwa birane.
Taron ya kasance dandalin tattaunawa da mu'amala mai karfi, inda ya bayyana irin gyare-gyaren da kasar Sin ke aiwatarwa, da tasirinsu a duniya, wanda ya nuna muhimmancin ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya, wajen cimma muradun ci gaba na bai daya. (Yahaya)