Me ya sa Hamas da Fatah suka iya samun sulhu tsakaninsu karkashin shiga tsakanin kasar Sin?
2024-07-25 21:59:37 CMG Hausa
DAGA MINA
Ran 23 ga wata, bangarori 14, ciki har da kungiyoyin Fatah da Hamas na Palasdinu sun gudanar da shawarwari a birnin Beijing na kasar Sin, har ma sun sa hannu kan Yarjejeniyar Beijing, wadda ke bukatar dinke baraka da wanzar da hadin kan Palasdinawa. Shawarar ta tabbatar da cewa, kungiyar ’yantar da al’ummar Plasdinawa wato PLO ita kadai take da ikon wakiltar al’ummar Palasdinu, kuma an kai ga cimma matsaya daya kan yadda za a kula da harkokin zirin Gaza bayan kawo karshen yaki da kafa gwamnatin sulhunta al’umommin kasar na wucin gadi.
An cimma nasarar samun sulhu tsakanin mabambantan bangarorin Palasdinu, karkashin shiga tsakanin kasar Sin, wanda da ma an yi hasashen cewa, abin maras yiwuwa ne. To, me ya sa Hamas da Fatah wadanda suka yi gaba da juna har tsawon shekaru 18, suka zabi Beijing don yin shawarwari tare da kulla yarjejeniyar sulhu?
Da farko, kasar Sin ta cimma nasarar shiga tsakanin Saudiyya da Iran, wadanda suka cimma matsaya daya a Beijing a bara, abin da ya samar da gudunmowa ga kokarin wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, inda nasarar ta baiwa mabambantan bangarorin Palasdinu kwarin gwiwa game da rawar da kasar Sin za ta iya takawa. Na biyu, Sin tana tsaya tsayin daka kan kiyaye zaman lafiya da kare mutuncin bil Adam, ba ta nufin cin ko wata moriya daga lamarin, tana yunkurin wanzar da zaman lafiyar shiyya-shiyya da na duk fadin duniya baki daya, matakin da ya samu amincewa daga sauran kasashe.
Wanzar da zaman lafiya da samun bunkasuwa abubuwan ne mafi muhimmanci da mutanen duk fadin duniya ke darajantar, saboda haka na yi imanin cewa, tabbas za a samu karin damammakin daidaita rikice-rikice iri daban-daban a Beijing nan gaba. (Mai zane da rubutu:MINA)