logo

HAUSA

An kaddamar da zauren kasar Sin a birnin Paris gabanin wasannin Olympics da za a fara

2024-07-25 11:03:42 CMG Hausa

A gabannin gasar wasannin Olympics da za a gudanar da birnin Paris, an kaddamar da zauren kasar Sin a jiya Laraba a Hotel Salomon De Rothschild da ke birnin, kuma daga ranar har zuwa ranar 10 ga watan Agusta, zauren zai kasance dandalin da za a yi musaya tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya kan harkokin wasannin motsa jiki, da ma dandali na yayata al’adun kasar Sin da karfafa mu’amala a tsakanin Sin da ketare.

Zauren kasar Sin wani dandali ne da kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar Sin ya kafa ga tawagar ‘yan wasan kasar da ke halartar gasannin kasa da kasa, wanda yake taka rawa ta fannonin samar da hidimomi da cudanya tsakanin al’ummomi da yayata al’adu da sauransu. (Lubabatu)