logo

HAUSA

Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

2024-07-25 19:31:45 CMG Hausa

A watannin 6 na farkon shekarar bana alkaluma sun tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da farfadowa da bunkasa bisa daidaito. Kaza lika, a ranar 16 ga watan nan ma asusun IMF ya fitar da sabon hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya, wanda ya nuna yiwuwar bunkasar tattalin arzikin kasar Sin da kaso 5 bisa dari a bana, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 0.4 bisa dari kan hasashen da asusun ya fitar a watan Afrilun da ya gabata.

Masharhanta na cewa wannan hasashe na bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, zai samar da karsashi na dogon lokaci ga farfadowa, da bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya. IMF dai ya amince cewa bunkasar tattalin arzikin kasashen Asiya masu samun saurin ci gaba ciki har da Sin, shi ne jigon bunkasar tattalin arzikin duniya, musamman a gabar da tattalin arzikin Sin ke kara habaka ta fuskar yawa da kuma inganci.

Alkaluma sun nuna cewa a wa’adin watanni 6 na farkon shekarar nan ta 2024, ma’aunin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin na GDP ya karu da kaso 5 bisa dari, inda darajarsa ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 61.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 8.49. Tsakanin wannan wa’adi, adadin sayayyar kayayyakin bukatun al’umma a kasar ta Sin, da hidimomi masu nasaba da hakan duk sun karu, yayin da jarin da ake kara zubawa a fannin samar da ababen more rayuwa ya daga da kaso 5.4 bisa dari kan na makamancin lokaci na bara.

Karin sassan dake bunkasa sun hada da na sarrafa hajoji a masana’antu, da cinikayyar waje, wadda a wannan wa’adi darajarta ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 21.2. Bisa dukkanin shaidu, tun daga mahanga ta kusa har zuwa tsawon lokaci mai zuwa, sassan tattalin arzikin kasar Sin za su ci gaba da bunkasa, yayin da kasar ke kara samun bunkasuwa mai inganci.

Idan an yi duba na tsanaki, abu ne mai sauki a gano dalilan da suka haifar da wannan nasara da kasar Sin ke samu. Ga misali bunkasar sarrafa hajojin masana’antu masu kunshe da fasahohin zamani, da sarrafa hajoji ba tare da gurbata muhalli ba sun taka rawar gani wajen ingiza tattalin arzikin kasar Sin.

Kaza lika fannin bunkasar sabbin fannonin samar da hajoji irin su kayayyaki masu amfani da kirkirarriyar basira, da fasahar sarrafa manyan bayanai, da hidimomin sayyaya ta yanar gizo, dukkaninsu sun baiwa kasar damar cin karin gajiya.

Har ila yau, kwazon kasar Sin na zurfafa gyare-gyare a dukkanin fannoni ya samar da sabon karfi na ingiza ci gaba mai inganci, da nasarar matakan zamanantarwa irin ta Sin. Masana da masharhanta sun yi imanin cewa tattalin arzikin kasar Sin zai sauya daga tsohon matakinsa zuwa sabon salo mai inganci, karkashin manufofin zurfafa gyare-gyare da kara bude kofofin kasar ga kasashen waje.

Yayin da ake fatan cimma nasarar hakan, kasar Sin ta wanzar da alakar cinikayya da sama da kasashen duniya da yankuna 140, wanda hakan ya sanya jimillar hada hadar hajojin kasuwancinta da kasashen waje ya kai matsayin farko a duniya cikin shekaru 7 a jere.

Bugu da kari, shawarar “ziri daya da hanya daya” ko BRI da kasar Sin ta gabatar ita ma na taka rawar ganin wajen dinke kasar da sauran sassan duniya ta fuskar cimma moriyar juna, inda kawo yanzu sama da kasashen duniya 150, da hukumomin kasa da kasa 30 suka shiga wannan shawara mai riba.

Masharhanta na ganin wannan ci gaba da Sin ke samu, dama ce ta musamman ga daukacin duniya ta morewa fasahohin Sin, da cimma moriyar juna, ta yadda dukkanin sassan duniya za su hada gwiwa domin a gudu tare a tsira tare. (Saminu Alhassan)