logo

HAUSA

Yawan hatsi da Sin ta samu ya zarce kg biliyan 650 cikin shekaru 9 a jere

2024-07-25 21:24:43 CMG Hausa

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai kan sa kaimi ga inganta bunkasuwa a ranar 24 ga wata. A gun taron, jami’an ma’aikatar aikin gona da raya karkarar kasar Sin sun gabatar da bayanai kan yanayin raya karkara.

Rahotannin sun ce, yawan hatsin da kasar Sin ta samu ya daidaita a fiye da kilogiram biliyan 650 cikin shekaru 9 a jere. Haka kuma, ana ci gaba da gina kauyuka masu kyau kuma masu dacewa da rayuwa. A halin yanzu,  yawan dakunan bayan haya masu tsafta da aka samar a yankunan karkara ya kai kusan kashi 75 cikin dari, yawan ruwan famfo da aka samar ya kai kashi 90 cikin dari, kuma adadin kauyuka masu hidimar wayar salula na 5G ya zarce kashi 90 cikin dari. (Yahaya)