logo

HAUSA

Wakilan kasashen Afirka sama da 50 sun halarci taron da aka gudanar dangane da manufar taron JKS

2024-07-25 11:13:49 CMG Hausa

Sashen hulda da kasa da kasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) tare da kwamitin jam’iyyar reshen lardin Hunan sun gudanar da taro a jiya, domin yayata manufar cikakken zama na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20 da ya gudana a kwanakin baya, inda aka bayyana muhimman matakan da aka cimma a wajen cikakken zaman game da kara zurfafa gyare-gyare daga dukkan fannoni da ma sa kaimin ayyukan zamanintar da kasar Sin. Taron ya samu halartar baki sama da 200 daga kasashen Afirka fiye da 50.

Bayan sauraron bayanan da jami’ai da masana suka yi, baki mahalarta taron sun bayyana cewa, cikakken zama na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20 ya tsara sabuwar taswirar bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma a kasar Sin, wanda yake da matukar muhimmanci a kokarin da kasar Sin ke yi na zurfafa gyare-gyare, haka kuma yake da matukar ma’ana ga kasar Sin da ma duniya baki daya. Sun ce yadda ake zamanintar da kasar Sin tabbas zai samar wa kasashen Afirka karin damammaki da kuma abubuwan koyi. Kasashen Afirka na fatan kara inganta musaya da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kan gudanar da harkokin mulki, da kuma zamanintar da kansu cikin hadin gwiwa, don gina al’ummar Sin da Afirka mai kyakkyawar makoma ta bai daya.