logo

HAUSA

Xi Jinping: Gasar Olympics alama ce ta hadin gwiwa da zumunci da ci gaban da aka samu ta fuskar koyi da juna a bangaren al’adu

2024-07-25 15:35:05 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron a fadar Élysée dake Paris hedkwatar kasar Faransa yau watanni 2 da suka gabata. Kafin shawarwarinsu, matan shugabannin biyu sun baiwa juna tsaraba.

Xi Jinping ya ba Macron wutar yola ta Olympics ta birnin Beijing, yayin da Macron ya mayar masa wutar yola ta Olympics ta birnin Paris. Xi Jinping ya ce, Faransa kasa ce mai karfin wasannin motsa jiki, kuma yana fatan za a cimma nasarar gudanar da gasar yadda ya kamata. Ya ce Sin za ta tura tawagoginta mafiya kwarewa zuwa gasar.

Xi Jinping ya dade yana mai da hankali kan harkokin wasan motsa jiki, dake zama gadar kara dankon zumuncin kasa da kasa da mu’ammalar jama’ar kasashe daban-daban, kuma yana dukufa kan inganta sha’anin Olympics, da ma ci gaba da hanzarta kafa kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya.

Xi Jinping na da alaka mai zurfi da gasar Olympics duba da cewa, ya zama shugaban rukunin share fagen gasar Olympics da gasar masu bukata ta musamman ta Beijing a shekarar 2008, da aiwatar da aikin neman iznin shirya gasar Olympics ta lokacin hunturu da gasar masu bukata ta musamman a Beijing a shekarar 2022, tare da cimma nasarar gudanar da su.

Yayin da Xi Jinping ya yi ziyarar aiki a kasar Faransa a watan Mayun bana, ya bayyana cewa, “gasar Olympics, alama ce ta hadin gwiwa da zumunci da kuma ci gaban da aka samu ta fuskar koyi da juna a bangaren al’adu”, kalmomin da ya fadi sun bayyana mutuntawarsa ga mabanbantan al’adu da nagartattun abubuwan dake kunshe cikin ruhin Olmpics, wato amincewa da juna da zumunta da hadin gwiwa da dai sauransu. (Amina Xu)