logo

HAUSA

CMG ya gudanar da tattaunawa kan “Zurfafa gyare-gyare a Sin dama ce ga duniya” a Afirka ta Kudu da Zambiya

2024-07-25 19:05:16 CMG Hausa

A ranar 24 ga watan Yuli agogon kasar Afirka ta Kudu, an gudanar da taron tattaunawa tsakanin kasa da kasa kan “Zurfafa yin gyare-gyare a kasar Sin dama ce ga duniya” wanda CMG ya shirya a birnin Johannesburg. Kuma shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Shen Haixiong ya bayyana cewa, kwanan nan aka yi nasarar kammala cikakken zama karo na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20 a birnin Beijing, wanda ya jawo hankalin duniya baki daya.

Wannan wani gagarumin ci gaba ne ga kasar Sin a sabon zamani. CMG ya himmatu wajen ba da labaran gyare-gyaren kasar Sin da bude kofa ga waje, da ba da labaran zamanantarwa irin ta kasar Sin, da yin aiki tukuru wajen gina gada ta cudanya da mu'amala, da tattaunawa, da fahimtar juna, da tuntubar juna tsakanin Sin da kasashen duniya.

Kazalika a wannan rana, CMG ya yi nasarar gudanar da taron tattaunawar a birnin Lusaka na kasar Zambiya. (Yahaya)