Sin da Rasha za su fadada hadin gwiwa a bangarorin zuba jari da makamashi
2024-07-25 15:07:49 CMG Hausa
Sin da Rasha sun lashi takobin zurfafa hadin gwiwarsu a bangarorin zuba jari da makamashi, da kuma kara kyautata dangantakarsu.
An cimma wannan matsaya ce biyo bayan jerin tarukan manyan jami’an bangarorin biyu da suka gudana a baya bayan nan.
Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang ya ziyarci Rasha daga ranar Lahadi zuwa jiya Laraba, inda ya halarci taro na 11 na kwamitin Sin da Rasha kan zuba jari da taro karo na 21 na kwamitin kasashen kan hadin gwiwa a bangaren makamashi, da kuma taro karo na 6 na dandalin tattauna harkokin kasuwancin makamashi tsakanin Sin da Rasha.
Yayin jagorantar tarukan tare da bangaren Rasha, Ding Xuexiang ya nanata muhimman yarjejeniyoyi da tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin kasashen biyu, yana mai cewa tattaunawar ta samar da sabuwar taswirar raya dangantakar kasashen biyu da hadin gwiwarsu a bangarori da dama.
Bangaren Rasha ya jinjinawa kyautatuwar dangantakar dake tsakaninsa da Sin da ma nasarorin da aka samu daga hadin gwiwarsu, ya kuma taya murnar nasarar gudanar da cikakken zama na 3 na kwamitin kolin JKS karo na 20. Yana mai cewa, kudurin da aka yanke yayin zaman, game da zurfafa gyare-gyare ba ci gaba da wadata kadai zai samar ga Sin ba, har ma da samar da sabbin damarmakin raya huldar Sin da Rasha. (Fa’iza Mustapha)