Tunawa da zakaran gasar Olympic Eric Liddell bisa sadaukar da rayuwarsa ga kasar Sin
2024-07-25 21:02:40 CMG Hausa
Nan da ‘yan kwanaki ne za a bude gasar Olympic ta birnin Paris ta shekarar 2024, wanda hakan ke nuni da cewa, gasar ta sake komawa birnin Paris bayan karni guda.
A shekarar 1924, an gudanar da sabbin tsare tsare da dama yayin gasar ta birnin Paris, ciki har da kaddamar da taken nan na gasar Olympic, wato "Sauri, daukaka, karfi", da batun samar da kauyen wasannin Olympic. A daya hannun kuma, a gasar ne aka fitar da zakarun gasanni daban daban, irin su dan wasan kasar Finland Paavo Nurmi, wanda ya lashe lambobin zinari har guda 5.
To sai dai kuma a bangaren kasar Sin, babban tauraronta yayin gasar ta Olympics ta birnin Paris a 1924, na iya kasancewa dan wasan tsere daga Birtaniya Eric Liddell. Kuma ba wai domin ya lashe lambar zinari a gasar tseren mita 400 kadai ba ne, ko don an yi amfani da tarihin rayuwarsa wajen hada fim din "Chariots of Fire", wanda ya lashe lambar yabo ta Oscar ba, sai don cewa an haife shi a kasar Sin, ya kuma sadaukar da dukkanin rayuwarsa a kasar ta Sin.
Sunan Eric Liddell na Sinanci shi ne Li Airui. An baje kolin abubuwan da suka shafi rayuwarsa, da nasarorin da ya cimma a gidan adana kayan tarihi na wasanni dake birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin.
Liddell, wanda iyayensa ‘yan asalin kasar Scotland ne an haife shi a birnin Tianjin a shekarar 1902. Kuma yana da shekara 5 aka mayar da shi Birtaniya domin yin karatu. Ya nuna hazaka sosai a fannin wasanni tun yana karami, inda a ko da yaushe yake kaiwa kusa da matsayin farko na gasannin tsere dake gudana a makarantarsa, kuma ya rike mukamin kyaftin a kungiyoyin wasannin “rugby”, da cricket na makaranta.
Bayan Liddell ya shiga jami’ar Edinburgh a shekarar 1920, sai kwazon sa a fannin wasanni ya kara bayyana, inda ya rika lashe lambobin yabo da dama a gasannin motsa jiki na kasa.
Liddell na cikin wadanda aka yi zaton za su iya lashe lambar zinari a tseren mita 100 yayin gasar Olympics ta Paris ta shekarar 1924. To sai dai yayin da jadawalin wasannin na Olympic ya nuna za a yi tseren daidaikun ‘yan wasa na mita 100, da na karba karaba na ‘yan tsere 4 a ranar Lahadi, sai Liddell ya janye daga halarta, kasancewa sa mai matukar bin addinin kirista, kuma Lahadin ranar zuwa bauta ce, maimakon wadannan wasanni sai ya yanke shawarar shiga gasa biyu, wato tseren mita 200 da na mita 400, duk da ba sa cikin tseren da ya fi son yi, kuma a lokacin ‘yan watanni kalilan suka rage masa ya yi atisaye kafin gudanar da su.
Amma fa duk da hakan, Liddell ya ba da mamaki, inda ya yi nasarar lashe lambar tagulla a tseren mita 200, tare da karya matsayin bajimta a tseren mita 400, inda ya kammala tseren a cikin dakika 47.06 ya kuma lashe lambar zinari a tseren.
Sakamakon wannan nasara, Liddell ya samu yabo da jinjina daga sassan daban daban. Bayan nan ne kuma, yayin da yake tsaka da haskakawa a fagen wasannin tsere sai ya bayyana aniyar yin wani abu da ya baiwa kowa mamaki, wato bayan kammala digirin farko a fannin kimiyya yana da shekaru 23 a duniya, sai ya yanke shawarar komawa birnin Tianjin, wato mahaifarsa domin ci gaba da zama a can.
Yar zuwa yanzu, mutane da dama sun kasa gane dalilin wannan mataki na Liddell. Ko da yake Zhao Yan, ma’aikaci a gidan adana kayan tarihi na wasanni dake birnin Tianjin, ya ce mai yiwuwa hakan ba ya rasa nasaba da dalilai biyu: Na farko burin Liddell na kasancewa tare da iyalansa, kasancewar iyayen sa suna zaune a Tianjin a lokacin, kana na biyu amincewar da ya yi cewa rayuwarsa za ta fi ma’ana, idan yana zaune a kasar Sin. Kamar yadda ya taba fada, "Tun daga haihuwa har zuwa mutuwa, kowa na kan turba iri daya, sai dai kawai kowa na bin turbar ne da irin na sa salo, kuma hakan ne ke sanyawa ma’anar rayuwa ta banbanta."
Bayan komawarsa Tianjin, Liddell ya karbi aiki a matsayin malamin kimiyya, da ilimin motsa jiki a kwalejin majami’ar Ingila da Sin. Kana ya koyar da ilimin sarrafa sinadarai da lissafi, da kuma aikin zakulo dalibai masu fasaha domin horas da su, da kuma yayata ruhin Olympic.
Karkashin jagorancinsa, makarantar da yake aiki ta samu damar kafa kungiyoyin kwallon kafa, da kwallon kwando, da baseball, da kwallon tebur, da tennis da volleyball, inda a lokacin makarantar ta yi fice wajen yaye dalibai masu hazaka sosai a fannin wasanni a birnin Tianjin.
Har ila yau, Liddell ya shahara, kasancewarsa Uba ga "Filin wasa na Minyuan", shahararren filin wasan dake birnin Tianjin a lokacin. A lokacin da aka sabunta gininsa a shekarar 1925, Liddell, ya bayar da shawarar tsara zanensa ta yadda ya yi kama da filin wasa na “Stamford Bridge” na Ingila, ya bayar da shawarwari a fannin tsarin gini, da sanya fitilu, da dandalin tsayuwar ‘yan wasa yayin ba da lambobin yabo, wanda hakan ya sanya filin wasan zama kan gaba wajen inganci a dukkanin nahiyar Asiya a lokacin.
A shekarar 1929, filin wasa na Minyuan ya karbi bakuncin gasar tsere ta kasa da kasa, inda Liddell ya doke dan wasan tsere daga Jamus wato Otto Pferz a tseren mita 500 ajin maza, inda ya lashe lambar zinari ta karshe a rayuwarsa.
A shekarar 1934, lokacin Liddell na da shekaru 32 ya auri Florence Mackenzie ‘yar kasar Canada a birnin Tianjin. Sai dai sakamakon barkewar yakin duniya na II, a shekarar 1941 Liddell ya tura matarsa wadda a lokacin ke dauke da juna biyu da sauran yaransu zuwa Canada, inda shi kuma ya ci gaba da zama a Tianjin, yana aiki cikin rukunin masu jinyar sojojin da suka yi rauni, tare da taimakawa ‘yan gudun hijira. A shekarar 1943, sojojin Japan suka kama Liddell tare da tsare shi a sansanin fursunonin yaki da a yanzu yake birnin Weifang na lardin Shandong.
A sansanin na fursunonin yaki, Liddell ya rika koyar da kimiyya da shirya wasannin motsa jiki, inda ya rika karfafawa ‘yan uwansa fursunonin yaki gwiwa, game da yadda za su zamo masu karfin hali. Sai dai duk da haka, tsawon lokaci da ya yi a tsare, da karancin abinci mai gina jiki ya yi matukar illata lafiyarsa. Inda a farkon shekarar 1945, Liddell ya rasu bayan ya sha fama da kari a kwakwalwa, yana da shekaru 43 a duniya.
Jama’a da dama sun rika jinjinawa labarin rayuwar Liddell a sassa daban daban na duniya, kuma a bana yake ciki shekaru 100 da lashe lambar zinari a gasar Olympics ta birnin Paris da ta gudana a shekarar 1924, inda aka gudanar da baje kolin abubuwa da dama da suka shafi tarihin rayuwarsa a sassa daban daban na duniya.