logo

HAUSA

Bola Ahmed Tinubu: Najeriya ba ta bukatar wata zanga-zanga a halin yanzu

2024-07-24 10:43:41 CMG Hausa

 

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci al’ummar kasar da su sauya shawara ta gudanar da zanga-zangar gama gari. Ya ce, yanzu Najeriya ba irin wannan mataki take bukata ba.

Shugaban ya bukaci hakan ne jiya Talata 23 ga wata bayan ganawar sirri da ya gudanar da ministan yada labaran kasar Muhammad Idris a fadarsa dake birnin Abuja, inda ya ce, zanga-zanga ba ta haifarwa kasa abun alheri illa sake jefa ta cikin yanayi mara tabbas.

Daga tarayyyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

A lokacin da yake yiwa manema labarai karin bayani a game da abun da suka tattauna da shugaban kasa, ministan yada labarai Ahaji Muhammed Idris ya ce, shugaban na tarayyar Najeriya yana sane da halin da al’ummar kasa suka tsinci kansu a cikin sakamakon sauye-sauyen manufofin tattalin arziki, wannan ce ta sanya shi kasa zama wajen bullo da tsare-tsare daban daban da za su kawo sauki rayuwa ga al’umma.

Ministan yada labaran ya ci gaba da cewa, gwamnati na bin komai sannu a hankali, inda ya bada misalin hanzartar zartar da kudurin dokar karin albashi ga ma’aikata, kuma akwai tsare-tsare da dama dake tafe wanda zai faranta ran al’ummar kasa.

“Shugaban kasa bai ga wani dalili na gudanar da wanann zanga-zanga ba, a don haka ya bukaci masu shirya zanga-zangar da su jingine wannan yunkuri nasu, su baiwa gwamnati damar nazartar dukkannin korafe-korafen da suka gabatar mata.” (Garba Abdullahi Bagwai)