logo

HAUSA

Me ya sa aka yi taron sulhu tsakanin mabambantan bangarori na Palasdinu a Beijing?

2024-07-24 14:37:12 CMG Hausa

 

Bangarori 14 na Palasdinu sun kulla yarjejeniyar dinke baraka da wanzar da hadin kan al’ummar Palasdinu a jiya Talata a Beijing, bayan sun gudanar da shawarwarin neman sulhu a tsakaninsu daga Lahadi zuwa Talatar nan. Sanarwar ta tabbatar da cewa, kungiyar ’yantar da al’ummar Plasdinawa wato PLO ita kadai take da ikon wakiltar al’ummar kasar, kuma an kai ga matsaya daya kan yadda za a gudanar da harkokin Gaza bayan yaki da kafa gwamnatin sulhuntawar al’umommin kasar na wucin gadi.

Da wuya aka samu ci gaba mai armashi wajen wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, abin da ya baiwa al’ummar Palasdinawa wadanda suke fama da yake-yake makoma mai haske. A madadin sauran bangarorin, shugaban tawagar Fatah Mahmud Alul da shugaban tawagar Hamas Mousa Mohammed Abu Marzook sun yi jawabi, inda suka gode da taimakon da Sin ta dade tana baiwa Palasdinu ba tare da wani sharadi ba, kuma suna jinjinawa matakin da Sin take dauka na nacewa ga adalci kan abubuwan dake shafar mata a duniya.

To, me ya sa bangarori daban-daban na Palasdinu suka sake zabar Beijing domin yin shawarwarin neman sulhu tsakaninsu? Dalili shi ne Sin ba ta da nufin cin moriyarta daga wannan batu, tana tsayawa kan wanzar da zaman lafiya da mutuncin bil Adam. Tun daga watan Augusta, lokacin barkewar rikici a sabon zagaye, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana matsayin da Sin take dauka sau da dama, wato dakatar da bude wuta nan da nan da hana yaduwar rikicin da ma nanata cewa, tsarin kafa kasar Palasdinu da Isra’ila shi ne hanya daya tilo da za a bi wajen warware wannan matsala a duk fannoni, kuma cikin adalci da dorewa.

Saudiyya da Iran sun kai ga matsaya daya a Beijing, zuwa yanzu bangarorin daban-daban na Palasdinu sun sanya hannu kan yarjejeniya, wadannan ci gaban da aka samu na alamanta cewa, Sin na yin iyakacin kokarin ba da taimako wajen wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya da samun bunkasuwa. Sin sahihiyar abokiya ce da kasashen Larabawa ke iya dogaro da ita. Hakan ya sa, abun da Sin take yi ke  samun amincewa daga bangarori daban-daban dake bukatar shiga tsakani har su kai ga matsaya daya, wanda da ma an yi hasashen cewa abu ne mara yiwuwa. (Amina Xu)