Sin ta nuna jajenta ga Habasha kan bala’in zaftarewar kasa da ya faru a kasar
2024-07-24 20:03:06 CMG Hausa
Yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta gudanar da taron manema labarai.
Game da bala’in zaftarewar kasa da ya faru a Habasha, Mao Ning ta bayyana cewa, Sin ta nuna jajenta ga hakan, ta mika ta’azziya ga mutane da suka rasu a cikin bala’in. Bangaren Sin yana so ya ba da taimakonsa a fannonin yaki da bala’in da aikin farfadowa bisa bukatun bangaren Habasha.
Game da batun bangarori 14 na Palasdinu da suka gudanar da shawarwari na neman sulhu tsakaninsu da kuma sa hannu kan yarjejeniyar Beijing a birnin Beijing, Mao Ning ta ce, bangaren Sin ba shi da moriyar kansa a batun Falasdinu. Yana dora muhimmanci kan adalci, kuma yana goyon bayan al’ummar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya don daukar makomarsu a hannunsu.
Dangane da ziyarar da wasu gungun manyan jami'ai na kamfanonin Amurka da dama suka kawo kasar Sin a baya-bayan nan, Mao Ning ta ce, matakan gyare-gyaren da kasar Sin ta dauka sun samar da karin sabbin damammaki ga kasar Sin wajen zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da samun ci gaba tare da sauran kasashen duniya.(Safiyah Ma)