logo

HAUSA

Babban bankin Nijeriya ya kara kudin ruwa zuwa kaso 26.75

2024-07-24 11:14:03 CMG Hausa

Babban bankin Nijeriya, ya sanar da kara kudin ruwa da maki 50 zuwa kaso 26.75, domin shawo kan hauhawar farashi da ya ki yin sauki a kasar mafi yawan al’umma a Afrika.

Gwamnan babban bankin Yemi Cordoso, wanda shi ne shugaban kwamitin kula da manufofin kudi, ya ce an dauki wannan mataki ne wanda ya zo watanni biyu bayan an kara kudin ruwan zuwa kaso 26.25, saboda tasirin karuwar farashin kayayyakin amfanin gida da na harkokin kasuwanci a cikin gida, kuma wani mataki ne da ya wajaba domin shawo kan hauhawar farashin.

Yemi Cordoso ya shaidawa manema labarai bayan taron kwamitin kula da manufofin kudi da aka yi jiya a birnin Abuja cewa, cikin nazarinsa, kwamitin ya lura da ci gaba da karuwar farashin kayayyakin abinci, lamarin dake ci gaba da yin tarnaki ga daidaton farashi. Haka kuma, kwamitin ya lura cewa, yayin da manufar ke daidaita bukatun kayayyaki da hidimomi, karuwar hauhawar farashin abinci da na makamashi na ci gaba da yin matsi kan daidaiton farashi.  (Fa’iza Mustapha)