logo

HAUSA

Sin ta shawarci kasashen da suka mallaki makaman nukiliya kada su yi amfani da shi wajen kaiwa juna hari

2024-07-24 14:30:46 CMG Hausa

 

Shugaban tawagar Sin, kana darektan sashen kayyade jan damara na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sun Xiaobo ya ce, Sin na shawartar kasashe 5 dake mallakar makaman nukiliya, da su sa hannu kan yarjejeniyar hana kaiwa juna hari ta amfani da makaman nukiliya da farko, ko ba da sanarwa mai alaka da hakan, da zummar rage kalubalen tada yake-yake ta amfani da makaman nukiliya a wasu muhimman yankuna. Yana mai cewa Sin ta gabatar da shawararta game da daftarin da abubuwa da za a sanya cikin wannan yarjejeniya.

Sun Xiaobo ya bayyana haka ne jiya, yayin jawabinsa a muhawarar taron share fage karo na biyu na babban taron sauraro da nazarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya karo na 11 da ake yi a Switzerland.

A cewarsa, Sin na kira ga al’ummun duniya da su aiwatar da matsaya daya da aka cimma game da rage makaman nukiliya, wato kasashe 2 mafiya karfin makaman nukiliya, su sanya sauke nauyin dake bisa wuyansu yadda ya kamata a gaban komai, kuma kada su bi hanyar da ba ta dace ba. Ya ce Sin na kalubalantar Amurka ta yi watsi da shirinta na sayar da makaman nukiliyarta ga kawayenta da ma amfani da makaman wajen ba su kariya, da janye makaman da ta girke a ketare da yin watsi da shirin girke na’urorin kakkabo makamai masu linzami a duniya, da dakatar da girke na’urar kakkabo makamai masu linzami ta LRHW a yankin Asiya da Pacific.

Wakilin na Sin ya kuma jaddada cewa, Sin ta kan tsaya kan matsayin hana yaduwa da murkushe makaman nukiliya a dukkan fannoni a duniya, kuma ta yi alkawarin ba za ta yi amfani da irin wannan makami wajen kai hari da farko ba, kuma ba za ta yi amfani da makaman kan kasashe da yankuna da ba su da makaman nukiliya ba. (Amina Xu)