logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin a Nijar ya gana da ministan lafiya na Nijar

2024-07-24 19:03:10 CMG Hausa

Jiya Talata, jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijar Jiang Feng ya gana da ministan lafiya, al'umma gami da zamantakewar al'umma na kasar Nijar Garba Hakimi, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi kan hadin gwiwar kasashen biyu a bangaren lafiya.

Yayin ganawarsu, jakada Jiang na kasar Sin ya ce, fannin aikin jinya da kiwon lafiya na daya daga cikin muhimman fannonin hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijar, inda kasar Sin ta aike da tawagogin likitoci 24 zuwa Nijar. Kana kasar na son yin aiki tare da kasar Nijar, da habaka fannonin hadin gwiwarsu a kai a kai, gami da taimakawa Nijar wajen inganta ayyukan likitanci.

A nasa bangaren minista Garba Hakimi ya darajanta zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasashen biyu, ya kuma nuna jin dadinsa da godiya ga kasar Sin bisa gagarumin taimakon da take baiwa Nijar a fannin aikin likitanci da kiwon lafiya. (Bello Wang)