logo

HAUSA

Yadda manufar kara yin gyare-gyare na kasar Sin za ta kawo wa kasashen Afirka damarmakin samun ci gaba

2024-07-24 08:53:38 CMG Hausa

A ranar 21 ga wata ne aka an fitar da cikakken bayanin ‘Shawarar da kwamitin kolin JKS ya yanke kan zurfafa gyare-gyare da sa kaimi ga zamanantarwa irin ta kasar Sin” wanda cikakken zama na uku na kwamitin kolin JKS karo na 20 ya yi nazari tare da amincewa da shi, wanda ya gabatar da shiri na musamman kan batun bude kofa ga kasashen waje. Manazarta na ganin cewa, hakan na dauke da wata alamar da ta nuna cewa, kasar Sin za ta fadada bude kofarta ga kasashen waje, kuma sauye-sauyen da kasar ke yi za ta samar da karin moriyar bude kofa ga kasashen duniya.

Abin da kasar Sin ke morewa da duniya da farko, shi ne babbar kasuwa mai girman gaske. Kuma abu mafi mahimmanci shi ne, bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin na ci gaba daga tsarin bude kofa bisa matakan samar da hajoji zuwa bude kofa a matakin hukumomi kamar yin kwaskwarima ga dokoki, ka'idoji, da gudanarwa da bukatu. Kasar Sin ta tabbatar wa duniya ta a zahiri cewa, abin da take nema ba zamanantar da kanta kadai ba ne, sai dai zamanantar da duniya tare da samun ci gaba cikin lumana, da hadin gwiwar moriyar juna, da samun wadata tare. 

Manufar ta ce, "ya zuwa shekarar 2035, za a gama gina tsarin tattalin arzikin gurguzu mai inganci daga dukkan fannoni, da kara kyautata tsarin gurguzu mai siffar kasar Sin, gaba daya za a sabunta tsarin kasar da karfin mulkin kasar, da tabbatar da zamanantarwa bisa tsarin gurguzu." (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)