logo

HAUSA

Shugaban Brazil: Sin muhimmin abokin hulda ne wajen bunkasuwar tattalin arzikin Brazil

2024-07-24 19:07:47 CMG Hausa

Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, ya bayyana a ranar Litinin cewa, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Brazil, kuma kasar Brazil na fatan kulla sabuwar huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.

A wata ganawa da ya yi da manema labarai na kasashen waje, Lula ya amsa tambaya daga wakilin Xinhua, inda ya ce yana da niyyar neman kulla alaka mai dorewa da kasar Sin.

Shugaban na Brazil ya kara da cewa, a karon farko a matsayin bako, zai halarci taron dandalin hadin gwiwar tattalin arziki na Asiya da Pasifik, wanda za a yi a watan Nuwamba a birnin Lima na kasar Peru, inda ya ke shirin tattaunawa da jami'an kasar Sin kan yiwuwar Brazil ta shiga cikin shawarar ziri daya da hanya daya. (Yahaya)