Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da shugaban kasar Senegal
2024-07-24 21:41:39 CMG Hausa
A jiya Talata, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong ya kai ziyarar ban girma ga shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye a birnin Dakar.
Yayin ganawar, Chen Xiaodong ya bayyana cewa, a wannan kaka, za a gudanar da sabon taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a birnin Beijing na kasar Sin. Kasar Sin tana maraba da shugaba Faye da ya halarci taron a matsayinsa na shugaban kasa mai jagorancin taron na bangaren Afrika, da kuma kai ziyarar aiki a kasar Sin.
Shugaba Faye ya yabi dangantakar da ke tsakanin kasashen Senegal da Sin, inda ya ce, yana Allah-Allahr zuwa kasar Sin domin halartar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, da kuma gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin, da zummar zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2. (Bello Wang)