logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Borno da asusun UNICEF sun kulla yarjejeniyar samar da asusun shawo kan karancin abinci mai gina jiki ga yara

2024-07-23 09:31:25 CRI

Asusun lura da kananan yara na majalissar dinkin duniya tare da gwamnatin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun samar da wata gidauniya ta musamman da za ta shawo kan matsalolin karancin abinci mai gina jiki ga kananan yaran dake jihar.

A karshen makon jiya ne dai a birnin Maiduguri, wakilan gwamnatin jihar da kuma na asusun na UNICEF suka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna wadda ta haifar da kirkirar asusun da aka yiwa lakabi da asusun abinci mai gina jiki ga yara.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.